Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo na son tsaffin Shuwagabannin Najeriya su hada kai su juyawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari baya.
Obasanjo nason tsaffin Shuwagabannin su hada kai su fitar da sanarwar Allah wadai akan shugaban kasa, Muhammadu Buhari su yi Allah wadai dashi akan matsalar tsaron dake damun Najeriya.
Saidai tsohon shugaban kasa, Janar Yakubu Gowon ya ki baiwa Obasanjo hadin kai kan wannan aniya tasu.
Obasanjo ya tuntubi duka sauran tsaffin Shuwagabannin Najeriya inda yace su hada baki su yi Allah wadai da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari saboda matsalar tsaron kasarnan yayi yawa.
Jaridar Politics Nigeria data samo wannan rahoto daga fadar shugaban kasa tace amma bata samu jin abinda sauran tsaffin Shuwagabannin kasar sukace akan lamarin ba.
Obasanjo dai ya yi suna wajan yiwa gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari rubuce-rubucen budaddiyar wasika inda yakan jawo hankali akan wasu lamura ko kuma yayi Allah wadai da wani abu da a ra’ayinsa yake ga bai masa daidai ba.