Tsohon Shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa bai kamata a raba Najeriya ba, zamanta a matsayin kasa dsya yafi Amfani.
Yace yawanci manyan Kabilun Najeriya basuwa kananan Adalci. Yace idan Hausawa da Yarbawa da Inyamurai suna iya kafa kasashen su idan Najeriya ta rabe sauran kabilun ya zasu yi kenan?
Yace sauran kabilun za’a rika zalintarsu ne kawai ana muzguna musu idan aka raba Najeriya. Ya bayyana hakane a dakin karatunsa dake Ogun yayin ziyarar wata kabilar TIV ta kaimasa.
“If the Yoruba can stand as a country, if the Igbos and the Hausa/Fulani can stand as separate countries, where do we want the minority groups to be?
“Now, by virtue of the present situation, they are a little bit protected, but if Nigeria breaks up, they will be oppressed and exterminated.”