Wednesday, July 24
Shadow

Obasanjo Ya Ziyarci Uwargidan Shugaban Kasa Bayan ‘Yan Kwanaki An Hange Shi Sanye Da Hula Kalar Tambarin Tinubu

Obasanjo Ya Ziyarci Uwargidan Shugaban Kasa Bayan ‘Yan Kwanaki An Hange Shi Sanye Da Hula Kalar Tambarin Tinubu

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ziyarci uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu domin murnar bikin Sallah, ranar Litinin a Legas.

Mataimaki na musamman ga uwargidan shugaban kasa kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Busola Kukoyi, ne ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X tsohon shafin twitter.

Ziyarar ta zo ne kwanaki bayan da aka ga tsohon shugaban kasar a wani taron sanye da hula da kayan adon da ya yi kama da tambarin da ke kan hular Tinubu.

Karanta Wannan  Sunayen maza masu dadi

Wannan ci gaban ya haifar da martani daban-daban, yayin da wasu ‘yan Najeriya ke tunanin ko Obasanjo ya koma goyon bayan Tinubu.

A ci gaban zaben 2023, Obasanjo ya amince da Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), a matsayin na daya a kasar.

Tinubu ya ziyarci tsohon shugaban kasar a lokacin yakin neman zabe, amma Obasanjo bai bayyana goyon bayansa ga tsohon gwamnan jihar Legas ba.

Daga Abbas Yakubu Yaura

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *