Hadimar mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo akan harkokin shari’a, Dr. Bilkisu Saidu yta musanta zargin da akewa me gidanta cewa ofishinsa Kiristoci ne kawai ko kuma yarbawane kawai a cikinsa.
Tace ita kanta wadda Asalinta daga Sokoto take, alamace ta cewa wancan zargin da akewa Osinbajo ba gaskiya bane.
Bilkisu ta kuma kara da cewa ana hakan ne kawai dan bata sunan mataimakin shugaban kasar.
Tace akwai yarbawa musulmai da kuma wanda ba yarbawa ba dake hidimtawa Osinbajon.
Dan haka ta karyata waccan yamadidin da ake.