Kungiyar Inyamuran Najeriya ta Ohanaeze Ndigbo ta taya dan takarar shugaban kasa na Labour Party, Peter Obi murnar shekara 61.
Inda kungiyar ta bayyana cewa tsohon gwamnan Anambran adalin shugaba ne mai son cigaban matasa dama sauran al’ummar Najeriya bakidaya.
Kuma tace shi ba bai taba satar kudin gwamnati ba don koda ya sauka mulki ba a tuhume shi da satar ko kwabo ba, saboda haka suna bayan shi a zabe mai zuwa.