Victor Osimhen yayi nasarar ciwa Napoli kwallaye biyu bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, inda tazo daga baya ta lallasa Udinese daci 2-1.
Kwallon ta kasance ta 11 da tauraron dan wasan Najeriyar yaci a wannan kakar, yayin da nasarar Napoli tayi tasa yanzu makinta daidai dana AC Milan a saman tebirin gasar Serie A.
Osimhen ya zamo dan wasan Najeriya na farko dayaci kwallaye biyu a wasa guda a kakar wasa biyu ta gasar Serie A, kuma ya zamo dan Afrika na hudu daya yi hakan bayan George Weah, Samuel Eto da Mohamed Salah.