Dan majalisar wakilai dake wakiltar Tarauni daga Kano, Hafizu Kawu ya bayyana cewa, a zaben shekarar 2023, Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ne zabinsa.
Kawu ya bayyana hakane a ganawa da manema labarai a Kano, Ranar Litinin, kamar yanda Premium times ta ruwaito.
Yace idan dai mataimakin shugaban kasar ya fito takara to shine gwaninsa a 2023.
Yayi kira tlga Mataimakin shugaban kasar ya fito takara inda yace hakan zai taimaka wajan ci gaba da ayyukan da gwamnati me ci ke gudanarwa.