Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana ƙwarin guiwar jam’iyyar APC na samun nasarar lashe zaben shugaban kasa a 2023.
Bayan tantance shi a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa, Osinbajo ya ce APC ce kan gaba, yayin da aka tambaye shi kan ɗan takarar da babbar jam’iyyar PDP ta tsayar Alhaji Atiku Abubakar.
Kawo yanzu an tantance fiye da mutum 15 tun bayan da aka fara aikin tantance ƴan takarar na jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya.
Sauran waɗanda aka tantance sun hada da tsohon gwamnan Legas Bola Ahmed Tinubu da shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawan da ministan sufuri Rotimi Amaechi.
Tun da farko APC ta fitar da sunayen mutum 23 wadanda ta ce sune za ta tantance kuma nan gaba a yau ake sa ran kammala tantance ‘yan takarar.