Shahararren mawakin Najeriya, David Adeleke wan akafi sani da Davido ya bayyana cewa ‘yan jiharsa ta Osun ba zasu sayar yadda da wani magudin zabe ba.
Ya bayyana hakan ne a kafar sada zumunta ta Twittwer inda yace Osun ba Ekiti bace, saboda haka ba zasu sayarwa da wani dan takara kuru’unsu ba a zaben gwamna mai zuwa.
A zaben gwamnan jihar Ekiti da akayi a karehn makon dabata an amu labari cewa manyan yan takarar jihar sun sayi kuru’u sosai a zabe su.