Sunday, December 7
Shadow
Dalilin da yasa na yafewa Maryam Sanda shine ta nuna nadama sosai sannan tana nuna kyakkyawan hali a gidan gyaran halin da ake tsare da ita>>Shugaba Tinubu

Dalilin da yasa na yafewa Maryam Sanda shine ta nuna nadama sosai sannan tana nuna kyakkyawan hali a gidan gyaran halin da ake tsare da ita>>Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, dalilin da yasa ya yafewa Maryam Sanda laifin kashe mijinta, Bilyaminu Bello shine ta nuna nadama sosai. Premium times ta ruwaito cewa fadar shugaban kasar ta bayyana hakane a yayin da cece-kuce yayi yawa kan yafiyar da shugaban kasar yawa Maryam Sanda inda wasu ke cewa laifinta yayi muni sosai, bai kamata ace an yafe mata ba. Saidai duk da haka, fadar shugaban kasar tace har yanzu ana kan duba sunayen da shugaban kasar ya yafewa kamin sakinsu.
An sace wayar Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Kaduna

An sace wayar Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Kaduna

Duk Labarai
Rahotanni daga jihar Kaduna na cewa, an sace wayar Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar. Lamarin ya farune ranar Alhamis kamar yanda kafar Leadership ta ruwaito inda tace an sace wayar Kwamishinan, Hon. Barrister Sule Shu’aibu (SAN). Ne a wajan wani taro da ya halarta. Zuwa yanzu dai ba'a bayyana sunan barawon da yayi satar ba. Lamarin ya baiwa mutane mamaki ganin cewa a ko da yaushe Kwamishinan na tare da jami'an tsaro ko ta yaya har barawon ya samu damar sace masa waya? Har yanzu hukumomi a jihar Kaduna basu fitar da sanarwa kan lamarin ba.
Kalli Bidiyon: Mutane ku rika amfani da kwakwalwarku, Hadisai na cin karo da juna>>Inji Chizo Germany

Kalli Bidiyon: Mutane ku rika amfani da kwakwalwarku, Hadisai na cin karo da juna>>Inji Chizo Germany

Duk Labarai
Mawaki, Chizo Germany ya jawo hankalin mutane da cewa su yi hattara da Hadisai domin Hadisan na cin karo da juna. Ya kawo Misalai inda yace Akwai Hadisin da aka ce Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam yaki yiwa wani Sallah saboda ya mutu da bashi. Sannan yace akwai kuma Hadisin dake cewa Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ya rasu da bashi. https://www.tiktok.com/@chizo_1_germany/video/7561018447602224386?_t=ZS-90clINnlO40&_r=1
Kalli Bidiyon: Naji Soja Boy yayi sabuwar Waka me suna da Tif da Taya, saidai mutane sun ki sauraren wakar, muna nan muna Addu’ar kada Allah ya bashi abinda yake so>>Inji Malam Abdulrahman Umar Sautussunnah

Malam Abdulrahman Umar Sautussunnah ya bayyana cewa ya ji Soja Boy yayi sabuwar Waka me suna da Tif da Taya amma bata samu karbuwa ba. Malam yace Soja Boy na neman sunane amma sai Allah ya hanashi, ya na ta waka amma taki karbuwa. Malam yace suna nan sunata Addu'ar Allah kada ya bashi abinda yake so tunda lalata tarbiyyar 'ya'yan mutane ya saka a gaba. https://www.tiktok.com/@abdurrahmanumarr/video/7561864092777073941?_t=ZS-90ckBkeBWIC&_r=1
Matatar Dangote ta kara farashin man fetur

Matatar Dangote ta kara farashin man fetur

Duk Labarai
Matatar Man fetur din Dangote ta kara farashin man fetur dinta a gidan man MRS dake Abuja zuwa Naira 950 akan kowace lita. Rahotanni sun ce ranar Talatar data gabata, Gidan man na MRS dake Abuja na sayar da man sa akan Naira 851 kan kowace lita amma zuwa ranar Laraba sai aka ga sun canja farashi zuwa 950. Hakanan sauran gidajen man dake da alaka da Dangote irin su Ardova da Optima suma sun canja Farashin nasu zuwa sama. Daya daga cikin manajojin gidan man MRS ya shaidawa kafar Daily Post cewa, matatar man Dangote ta kara farashin da take sayarwa da 'yan kasuwa man.
Ana rade-radin cewa, Gwamnati ta soke Jarabawar JAMB, Gwamnatin ta yi martani

Ana rade-radin cewa, Gwamnati ta soke Jarabawar JAMB, Gwamnatin ta yi martani

Duk Labarai
Rahotanni sun watsu sosai cewa, Gwamnatin Tarayya ta soke jarabawar JAMB a matsayin ma'unin shiga jami'a. Saidai a martanin Gwamnatin ta bakin ministan Ilimi, Dr. Maruf Tunji Alausa CON, yace wannan labari ba gaskiya bane kuma ba daga hannunsu ya fito ba. Yace domin kawar da duk wata tantama, JAMB har yanzu itace jarabawar da dalibai zasu rika yi dam samun damar shiga jami'a. Yace kuma zasu ci gaba da hada kai da JAMB dan cimma burikan Ilimi.
Kalli Bidiyon: Ba kudi aka bani na yi ridda na koma Kirista ba, yanzu abu daya nake nema wajan Malaman Musulmai shine su nuna min inda aka cewa Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) yayi Sallah sau biyar a rana a cikin Qur’ani>>Inji Abubakar dan jihar Borno da yayi Ridda

Matashi Abubakar dan jihar Borno wanda yayi ridda ya koma Kirista ya bayyana cewa, ba gaskiya bane labarin da ake yadawa cewa kudi aka bashi ya koma kirista. Yace bincikene yayi ya gano gaskiya. Yace yanzu abinda yake so shine a samu malamai su nuna masa inda aka cewa, Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ya yi sallah sau biyar a Qur'ani. Yace idan aka nuna masa zai sake komawa Musulunci. https://www.tiktok.com/@winningsoulsminist/video/7561786035257068818?_t=ZS-90cR6JKMTA1&_r=1
Kalli Bidiyon:Munji Dadin Abinda Kwamitin Shura na Kano suka yi game da Malam Lawal Triumph, Yanzu muna jiransu su kira wadanda suka cewa Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) Raqumi da Hankaka suma su kawo hujja a litattafan da suka samo hakan>>Inji Shugaban Izala, Sheikh Bala Lau

Shugaban Izala, Sheikh Bala Lau yace sun ji dadin Abinda Kwamitin Shura na Kano suka yi akan malam Lawal Triumph. Yace sun jinjina musu, yace amma kuma suna jiran su ga an gayyaci wadanda suka kira Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) da Raqumi da kuma hankaka, kamar yanda malam Lawal Triumph ya bude littafi ya kawo hujja, suma su bude littafi su kawo Hujjar inda suka ga hakan. Yace idan kuwa ba a yi hakan ba to ba'awa Ahlussunah Adalci ba. https://www.tiktok.com/@taskarmalanlawantriumph/video/7561563264598035719?_t=ZS-90cQ5985Fx3&_r=1
Akwai yiyuwar Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai fasa yafewa Maryam Sanda bayan da cece-kuce yayi yawa akan yafiyar da aka ma

Akwai yiyuwar Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai fasa yafewa Maryam Sanda bayan da cece-kuce yayi yawa akan yafiyar da aka ma

Duk Labarai
Rahotanni sun ce akwai yiyuwar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai canja ra'ayi kan yafiyar da yawa wasu masu laifi dake tsare a gidajen yarin kasarnan. Yafiyar shugaban kasa ga masu laifi ana yintane dan rage cinkoso a gidajen yari musamman ga masu laifin da ake ganin bashi da tsauri sosai. Saidai bayan fitowar Jadawalin masu laifin da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya yafewa an ta cece-kuce musamman saboda ganin wasu sunayen manyan masu laifi da ake ganin bai kamata a yafe musu ba saboda munin laifukan da suka aikata. Babban lauyan Gwamnatin tarayya, Lateef Fagbemi (SAN) ya bayyana cewa, har yanzu ba'a kammala yafewa masu laifin ba, ana kan sake dunaba sunayen wadanda akawa yafiyar, inda yace bayan nan ne za'a gabatarwa da hukumar kula da gidajen yarin kasarnan dan a saki wad...