Sunday, December 7
Shadow
Kalli Bidiyon: Gwamnan jihar Naija ya jawo cece-kuce sosai bayan da aka ganshi ya shiga coci an yi irin addu’ar kiristoci dashi

Kalli Bidiyon: Gwamnan jihar Naija ya jawo cece-kuce sosai bayan da aka ganshi ya shiga coci an yi irin addu’ar kiristoci dashi

Duk Labarai
Gwamnan jihar Naija, Umar Bago ya jawo cece-kuce sosai bayan da aka ganshi a coci yana wakoki da addu'o'i irin na kirista. Gwamman ya shiga cocin Living Faith Church ne dan yin Addu'ar zaman lafiya. Wasu dai musamman 'yan Kudu sun rika cewa da talaka ne da watakila an dauki mataki akanshi. https://twitter.com/dammiedammie35/status/1978900420727611692?t=opFPHjWvCYxCu8By6niDvA&s=19
Me Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar II ya nemi Gwamnati ta yi dokar sanya ido a kafafen sadarwa saboda chin Mutuncin da ake yiwa manyan mutane yayi yawa

Me Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar II ya nemi Gwamnati ta yi dokar sanya ido a kafafen sadarwa saboda chin Mutuncin da ake yiwa manyan mutane yayi yawa

Duk Labarai
Me Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III ya nemi Gwamnati data yi sabuwar dokar da zata rika saka ido a kafafen sada zumunta saboda cin fuskar da akewa manyan mutane ta yi yawa. Hakanan ya bayyana cewa ana amfani da kafafen sada zumuntar dan barazanar tsaro. Yace amfani da kafafen sadarwa ta hanyar da bata kamata ba na barazana ga zaman lafiya, Girmama juna, da hadin kan kasarnan. Ya bayyana hakane ta bakin Me martaba sarkin Zazzau, Ahmad Nuhu Bamalli a wajan taron manyan malamai daya gudana a Kaduna wanda aka yi saboda tattauna matsalar tsaro da zaman takewa. Yace a wasu kasashen akwai dokar amfani da kafafen sadarwa ta yanda idan mutum ya saka sakon da bai kamata ba ko na cin zarafi za'a nemoshi a hukuntashi. Yayi kira ga mahukunta dasu dauki irin wannan mata...
Lura da irin Arzikin da Allah yawa Najeriya, bai kamata akwai talaka a kasarnan ba>>Inji Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu

Lura da irin Arzikin da Allah yawa Najeriya, bai kamata akwai talaka a kasarnan ba>>Inji Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, Lura da irin Arzikin ma'adanan karkashin kasa da Allah yawa kasarnan, bai kamata ace akwai talaka a kasarba Shugabab ya bayyana hakane a wajan taro kan Arzikin ma'danan karkashin kasa da Allah yawa Najeriya da ya gudana a Abuja. Sakataren Gwamnatin tarayya, George Akume ne ya wakilci shugaban kasar a wajan taron. Ya bayyana cewa, Gwamnatin tarayya zata yi dukkan mai yiyuwa wajan samar da yanayi me kyau na zuba hannun jari a kasarnan ta bangaren ma'adanan karkashin kasa. Sannan ya yi kira ga kasashen Afrika dasu yi amfani da ma'adannan karkashin kasar da Allah ya hore musu dan karfafa tattalin arzikin su.

Kwana hudu da suka gabata na musulunta, amma ana gayamin za’a koreni daga wajan aiki na idan ban bar Musulunci ba, Saidai na zabi Allah da Addinin Musulunci maimakon aikin nawa>>Inji Ba’amurke, Martin

Duk Labarai
Wani ba'amurke me suna Martin ya bayyana cewa, kwanaki 4 da suka gabata ya shiga addinin Musulunci. Yace amma kuma an matsa masa a wajan aikinshi cewa sai ya bar addinin Musulunci. Yace shi kuma ya zabi ya ci gaba da kasancewa a addinin Musulunci. ya wallafa hakane a shafinsa na sada zumunta. https://twitter.com/D_Maaartin/status/1978489878590406762?s=19
Farashin Man fetur ya kai Naira dubu(1000) kan kowace lita a yayin da Layuka suka fara tsawo a gidajen man fetur

Farashin Man fetur ya kai Naira dubu(1000) kan kowace lita a yayin da Layuka suka fara tsawo a gidajen man fetur

Duk Labarai
Rahotanni sun ce Laiyukan ababen hawa sun fara yawa a gidajen Man fetur a sassa daban-daban na Najeriya a yayin da ake fama da hauhawar farashin man a garuruwa daban-daban. Rahoton yace Farashin litar man fetur din ya kai Naira 1000. 'Yan kasuwar man fetur sun zargi Depot dake sayar musu man a farashin sari da cewa, sune suka sa man yayi tsada dan sun kara farashin da suke sayar musu da man. Hakan na zuwane duk da ga matatar man fetur ta Dangote a Najeriya kuma ya fara kai man fetur din zuwa wasu gidajen man kyauta ba kudin dako.
Lauyoyin Nnamdi Kanu sun bayyana cewa, basu yadda da Sakamakon gwajin Lafiyar da aka masa ba inda suka ce ko jininsa ba’a dauka ba ta yaya za’a ce yana da lafiyar da zai iya ci gaba da tsayawa a gaban kotu?

Lauyoyin Nnamdi Kanu sun bayyana cewa, basu yadda da sakamakon gwajin Lafiyar da aka masa ba inda suka ce ta yaya gashi an tabbatar bashi da lafiya amma ace wai zai iya tsayawa a gaban Kotu. Lauyoyin bayan zaman kotun a yau, Alhamis sun bayyana cewa, suna kira ga kungiyar Likitoci ta kasa data kiyaye kada ta batawa kanta suna. https://twitter.com/General_Somto/status/1978774791155806233?t=L8YzAemwn84Rd-Nqt73sww&s=19 A baya dai sakamakon da likitoci suka fitar akan Lafiyar Nnamdi Kanu sun ce zai iya ci gaba da tsayawa a gaban kotu dan ci gaba da masa shari'a sannan kuma Asibitin sha ka tafi na DSS zai iya ci gaba da dubashi saboda rashin lafiyar tasa bata yi tsanani ba.
Kalli Bidiyon: Wallahi ‘yan Darika 6 ne suka kirani suka ce sun Tuba sun daina Darika bayan da Malam Lawal Triumph ya kare kansa a gaban Kwamitin Shura>>Inji Malam

Kalli Bidiyon: Wallahi ‘yan Darika 6 ne suka kirani suka ce sun Tuba sun daina Darika bayan da Malam Lawal Triumph ya kare kansa a gaban Kwamitin Shura>>Inji Malam

Duk Labarai
Malam ya bayyana cewa, Bayan da Malam Lawal Triumph ya kare kansa a gaban Kwamitin Shura na Kano, akwai 'yan darika Guda 6 da suka kirashi suka ce sun daina Darika. Yace cikinsu hadda mace. Malam Yayi kira ga Gwamnan Kano da ya daina yadda ana sakashi a wannan rikicin inda yace ya barsu da 'yan Darikar su sun san yadda zasu yi dasu. https://www.tiktok.com/@ali_d_abba/video/7561178610330045718?_t=ZS-90b3UnM1PUn&_r=1
Wata Sabuwa, Kalli Bidiyon: Ana zargin Kudi aka baiwa matashinnan na Maiduguri ya yi Ridda ya koma Kirista

Wata Sabuwa, Kalli Bidiyon: Ana zargin Kudi aka baiwa matashinnan na Maiduguri ya yi Ridda ya koma Kirista

Duk Labarai
Matashinnan na Maiduguri da yayi ridda ya koma Kirista ya jawo cece-kuce sosai a kafafen sada zumunta. Wasu sun rika tambayar ko yana cikin hayyacinsa ya dauki wannan mataki? Saidai a nasa sharhin, Abdullahi yayi zargin cewa, Kudi aka baiwa matashin ya bar Addinin Musulunci. Saurari Sharhin Abdullahi a Bidiyon kasa https://www.tiktok.com/@abdallahtoyota0/video/7561065754917899528?_t=ZS-90b1uA5bpzM&_r=1