Sunday, December 7
Shadow
Ba sai an je da yawa ba, Shekaru 4 sun isheni in gyara Najeriya idan aka zabeni shugaban kasa>>Inji Peter Obi

Ba sai an je da yawa ba, Shekaru 4 sun isheni in gyara Najeriya idan aka zabeni shugaban kasa>>Inji Peter Obi

Duk Labarai
Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour Party a zaben shekarar 2023, Peter Obi ya bayyana cewa, shekaru 4 sun isheshi ya gyara Najeriya idan aka zabeshi shugaban kasa. Peter Obi ya kuma baiwa magoya bayansa tabbacin zai tsaya takarar shugaban kasa a 2027. Ya bayyana hakane a ganawar da yayi da manema labarai a Abuja ranar Laraba. Ya kuma ce yana da Kwarewa da cancantar zama shugaban kasa a Najeriya. Obi ya kuma bayar da tabbacin cewa, duka 'yan Najeriya dake son Najeriya da arziki zasu taru ne dan kayar da Gwamnati me ci.
Farashin kayan abinci ya sauka sosai wadda rabon a ga haka tun shekaru 3 kenan

Farashin kayan abinci ya sauka sosai wadda rabon a ga haka tun shekaru 3 kenan

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, alkaluman farashin kayan abinci ya sauka a Najeriya inda a yanzu yake a maki 18.02 a watan Satumba daya gabata. Idan aka kwatanta da watan Augusta daya gabata, Alkaluman na matsayin maki 20.12 wanda hakan ke tabbatar da an samu sauki sosai. Hukumar kula da kididdiga ta kasa, NBS ce ta bayyana hakan a sanarwar data fitar ranar Laraba. Rabon da makin na NBS ya sakko kasa da 20, shekaru 3 kenan.
Nnamdi Kanu na da lafiyar da zai iya fuskantar shari’a – Likitoci

Nnamdi Kanu na da lafiyar da zai iya fuskantar shari’a – Likitoci

Duk Labarai
Tawagar ƙwararrun likitoci a Najeriya, ƙarƙashin jagoranci shugaban ƙungiyar Likitocin ƙasar, sun tabbatar da cewa rashin lafiyar da aka ce na damun Nnamdi Kanu ba wata babbar damuwa ba ce. Maishari'a, James Omotosho ne ya umarci tawagar likitocin ta duba lafiyar Kanu, bayan da lauyoyinsa suka yi iƙirarin cewa yana fama da wata jinya. Cikin rahoton binciken tawagar ƙwararrun likitocin, da aka miƙa wa kotu ranar 13 ga watan Oktoban da muke ciki, ya ce rashin lafiyar da ke damun Kanu ba mai barazana ba ce. Tawagar likitocin ta ce bayan auna lafiyar Kanu sun tabbatar da cewa za a iya ci gaba da yi masa shari'a, domin kuwa zai iya halartar kotu. Bayan karɓar rahoton, Maishari'a Omotosho ya ce kotun ta gamsu da rahoton don haka za a ci gaba da shari'ar.
Kalli Bidiyo: Wasu matuka jirgin sama na Najeriya na shan Wiywiy, wani lokacin sai na hau jirgi idan na ga yanayin Direban sai in sauka saboda tsaro>>Inji Sanata Orji Uzor Kalu

Kalli Bidiyo: Wasu matuka jirgin sama na Najeriya na shan Wiywiy, wani lokacin sai na hau jirgi idan na ga yanayin Direban sai in sauka saboda tsaro>>Inji Sanata Orji Uzor Kalu

Duk Labarai
Sanata Orji Uzor Kalu ya bayyana cewa, da gaskene, Wasu matuka jirgin sama a Najeriya suna shaye-shayen wiwi. Yace wasu lokutan sai ya hau jirgi idan ya ga yanayin Matukin sai ya sauka saboda tsaro. Sanata Kalu ya zargi hukumomin dake kula da matuka jirgin da sakaci wajan kula da cewa basa shaye-shaye kamin su hau jirgi su tuka. Ya kuma bukaci a kula da titin da jirgin ke sauka wanda yace yana bukatar gyara. https://twitter.com/Imranmuhdz/status/1978719960982548642?t=XkSduGPf3oMEW1GFguNjKg&s=19 A kwanakin baya dai, An samu wani Matukin jirgin sama da Shan wiwi a Najeriya.
Kalli Bidiyon: Mazan Najeriya kuwa Allah ku daina Aikomin da sakon cewa kuna sona, Bature nake son in aura, Farar Fata, wanda zai kaini kasarsu>>Inji Wannan baiwar Allahn

Kalli Bidiyon: Mazan Najeriya kuwa Allah ku daina Aikomin da sakon cewa kuna sona, Bature nake son in aura, Farar Fata, wanda zai kaini kasarsu>>Inji Wannan baiwar Allahn

Duk Labarai
Wata baiwar Allah 'yar Najeriya ta gargadi matasan Najeriya da cewa, su daina damuna da sakonnin cewa suna sonta. Tace bata son Namiji dan Najeriya, Bature take so fari, me fata me laushi wanda zai samar mata da fasfo ya kaita kasarsu. Ta bayyana hakane a wani Bidiyonta da ya watsu sosai a kafafen sada zumunta kuma wadannan kalamai nata sun jawo zazzafar Muhawara. https://twitter.com/Teeniiola/status/1978461569324368341?t=gePpvcMbMHmfmVy5BmNd7Q&s=19
Ji yanda jami’in Kwastam ya riga mu gidan gaskiya a jihar Katsina bayan shiga dakin Otal da zaratan mata 3

Ji yanda jami’in Kwastam ya riga mu gidan gaskiya a jihar Katsina bayan shiga dakin Otal da zaratan mata 3

Duk Labarai
Rahotanni daga jihar Katsina sun bayyana cewa, wani jami'in Kwastam me suna Lawal Tukur me mukamin  Assistant Superintendent of Customs (ASC) ya rigamu gidan gaskiya a wani dakin Otal. Kafar Zagazola makamace ta wallafa labarin inda tace jami'in Kwastam din ya rasu ne a dakin Otal din Murjani Hotel ranar 15 ga watan October. Zagazola makama sun ce Ma'aikatan otal din sun tarar da gawar jami'in kwance a dakin da ya kama da misalin karfe 8:30 a.m. Zagazola makama sunce kamin rasuwarsa wasu mata 3 sun ziyarceshi a dakin, matan sune kamar haka, Khadija Ali me shekaru 34, wadda ta fito daga Dutsen Amare Quarters dake jihar ta Katsina, sai A'isha Lawal me shekaru 30 wadda ta fito daga karamar hukumar Ingawa, Sai Hafsat Yusuf me shekaru 22 wadda ta fìto daga Brigade Quarters j...
Kalli Bidiyon: Ba Alfahari ba, Mu Ahlussunah mune masoya Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) na gaskiya>>Inji Malam Lawal Triumph

Kalli Bidiyon: Ba Alfahari ba, Mu Ahlussunah mune masoya Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) na gaskiya>>Inji Malam Lawal Triumph

Duk Labarai
Malam Lawal Triumph ya bayyana cewa, Ahlussunah sune masoya Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) na gaskiya. Ya bayyana hakane yayin wani wa'azi da aka yi bayan Bayyanarsa a gaban Kwamitin Shura na Kano ya kare zargin da ake masa na munana kalamai ga Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam). Malam yace duk wanda yace wani musulmi baya son Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) to kamar ya kafurtashi ne dan son Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ginshiki ne a Musulunci. https://www.tiktok.com/@zaidou1taza/video/7561535409746988299?_t=ZS-90al84WfytM&_r=1
Kalli Bidiyon: A karin farko tun bayan da aka ce cutar shanyewar rabin jiki ta kamashi, An ga Ministan Kudi a Birnin Landan tsaye da kafafunsa

Kalli Bidiyon: A karin farko tun bayan da aka ce cutar shanyewar rabin jiki ta kamashi, An ga Ministan Kudi a Birnin Landan tsaye da kafafunsa

Duk Labarai
Ministan Kudi, Wale Edun ya bayyana a birnin Landan inda aka ganshi a tsaye da kafafunsa. Hakan na zuwane kwanaki kadan bayan da rahotanni suka watsu cewa bashi da lafiya kuma cutar Shanyewar rabin jiki ta kamashi. An ganshi a wajan wani bikin baje kolin fasahar zanezane da aka yi a landan din. https://twitter.com/Imranmuhdz/status/1978485657065455682?t=4MrhPuW4ub6nHj7ZXkcVxg&s=19
Babu Dan Siyasar da zai iya kayar da Tinubu a 2027>>Inji Fadar Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu

Babu Dan Siyasar da zai iya kayar da Tinubu a 2027>>Inji Fadar Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu

Duk Labarai
Fadar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta bayyana cewa babu dan siyasar da zai iya kayar da shugaban kasar daga mulki a zaben shekarar 2027. Me baiwa shugaban kasar shawara kan harkar sadarwa, Daniel Bwala ne ya bayyana haka a ranar Talata yayin ganawa da wasu kungiyoyin goyon bayan shugaba Tinubu su 100. Ya bayyana cewa, shugaba Tinubu ya kafu sosai a kowane sashi na kasarnan babu wanda zai iya kayar dashi zabe.
Kalli Bidiyo: Wasu daga cikin Musulmai na cin kazantacciyar Halitta, Alade, da shan Giyya da Mu’amala da mata masu zaman kansu>>Inji Alpha Charles Borno

Kalli Bidiyo: Wasu daga cikin Musulmai na cin kazantacciyar Halitta, Alade, da shan Giyya da Mu’amala da mata masu zaman kansu>>Inji Alpha Charles Borno

Duk Labarai
Tauraruwar Tiktok, Alpha Charles Borno ta bayyana cewa, a Kaduna akwai Wasu daga cikin musulmai dake cin nama kazantacciyar halitta, Alade. Tace kuma suna shan giya da mu'amala da matan banza. Ta bayyana hakane a matsayin martani da wani yace mata arna na cin Naman kare. https://www.tiktok.com/@alphacharlesborno/video/7560902313582316818?_t=ZS-90agmeAb4lN&_r=1