fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Paris saint German na harin siyan Karim Banzema daga Real Madrid dan ya maye gurbin Edinson Cavani

Karim Banzema ya kasance tsohon dan wasan gaba na Lyon, ya koma kungiyar Real Madrid a shekara ta 2009 yayin dan wasan mai shekaru 32 yayi nasarar lashe gasar champions lig har sau hudu kuma yaci kwallaye guda 150 na gasar La Liga.

 

Manema labarai na Mundo Deprotivo sun ce kungiyar Paris saint German suna harin siyan tauraron Madrid din domin ya maye masu girbin Edinson Cavani, saboda cavani yace zai bar kungiyar a kyauta da zarar kwantirakin shi ya kare a karshen wannan kakar wasan.
PSG suna fuskantar gagarumar matsala wajen siyan dan wasan saboda yana da matsayi a kungiyar yayin da yakai tsawon shekaru 11 yana wasa tare da su kuma zidane yana son shi sosai. Madrid suna harin siyan tauraron Tottenham Harry Kane da kuma zakaran Bayern Munich Robert Lewandowski.
Saboda haka ana sa ran idan suka yi nasarar siyan daya daga cikin yan wasan da suke hari to zasu iya barin Banzema ya koma kasar faransa ya cigaba da wasa a kungiyar PSG.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Da Dumi Duminsa: Elon Musk zai saya kungiyar Manchester United

Leave a Reply

Your email address will not be published.