fbpx
Wednesday, February 24
Shadow

PDP ta bukaci a gaggauta sauke Ministan Tsaro, saboda ya gayawa yan Najeriya su kare kansu daga yan bindinga

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta yi kira da a gaggauta sauke Ministan Tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi nan take, saboda ya kasa sauke nauyin da ke kansa ta hanyar neman ‘yan Nijeriya da ba su da makami su kare kansu daga hare-haren‘ yan bindinga da ‘yan ta’adda.

A cikin wata sanarwa da kakakinta, Kola Ologbodiyan ya fitar, babbar jam’iyyar adawar ta bayyana kalaman da ministan ya yi a matsayin sakaci, rashin kulawa da kuma tabbatar da cewa gwamnatin Buhari ta gaza tare da mika wuya ga yan ta’adda saboda bata iya dakatar da su.

Jam’iyyar ta kara da cewa a maimakon Ministan Tsaron yayi nazari sauya dabarun yakin da yan ta’adda amma yake umurtar yan kasa da su kare Kansa, bisa haka jami’iyyar PDP take Kira da a gaggauta sauke Ministan.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *