fbpx
Saturday, September 23
Shadow

PDP ta fara sasanci tsakanin Atiku da Wike bayan da suka halacci taron data gudanar a babban birnin tarayya

A yau ranar alhamis hudu ga watan Augusta jam’iyyar PDP ta gudanar da babban taro a Abuja wanda dan takararta na shugaban kasa Atiku da gwamnoni suka halatta.

Kuma gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike ya hallaci taron inda suka hadu dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar wato Atiku Abubakar.

Wani daga membobin jam’iyyar daya halacci taron ne ya bayyana hakan, kuma yace an hada taron ne don magance matsalolin da jam’iyyar ke fuskanta,

Da kuma hada kan Atiku da Wike wanda suka samu matsala a tsakaninsu tun bayan da jam’iyyar ta gudanar da zaben fidda gwani a watan Mayu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *