Tsohon datekta janar na sojojin dake kula da jiragen ruwa, Dakuku Peterside ya bayyana farin cikinsa akan yadda APC ta gudanar da babban taronta cikin limana.
Yayin da kuma yayi kira ga mutanen Najeriya cewa suyi APC sak daga kan shugaban kasa, gwamnoni dama sauran shuwagabanni bakidaya.
Inda kuma yayi kira mutanen Rivers cewa su fito su zabi APC domin su ceto kansu daga hannun azzalumar gwamnatin Nyesom Wike ta PDP.
A karshe ya kara da cewa dole PDP ta fadi zaben jihar a shekarar 2023 domin sun gaji kuma suna bukatar agaji daga wurin APC domin ta ceto al’ummar su.