fbpx
Tuesday, May 24
Shadow

PDP za ta sha kasa a zaben 2023 idan har ta tsayar da dan Arewa – Kungiyar Yarbawa (Ronu)

Wata kungiyar siyasa da zamantakewa ta Yarbawa mai suna Ronu, ta yi hasashen cewa jam’iyyar adawa ta PDP ba za ta samu nasara ba a zaben 2023 idan ta tsayar da dan takarar shugaban kasa a arewa.

Mambobin kungiyar Ronu, sun ce makircin da PDP ke yi na kin bari a tsaida dan takarar daga wani yankin da ba Arewa ba a zaben shugaban kasa zai sa su yi mummunar faduwa.

Kungiyar ta kara da cewa duk jam’iyyar da ta tsaida dan yankin kudu a matsayin dan takarar shugaban kasa, akwai alamun zasuyi gagarumar nasara domin yan Nageriya sun fi son a tsaida dan kudancin kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published.