fbpx
Tuesday, August 4
Shadow

Pele ya taya Cristiano Ronaldo murna bayan ya lashe kofin Serie A karo na biyu a jere

Zakaran kasar Brazil Pele ya taya Cristiano Ronaldo murna bayan Juventus ta lashe kofin gasar Serie A karo na tara a jere. Ronaldo da Federico Bernardeschi sune suka ciwa Juventus kwallaye biyu a wasan su da Sampdoria wanda yasa suka lashe kofin.

Nasarar da Juventus suka yi tasa yanzu Ronaldo ya lashe kofunan gasa guda bakwai a kungiyar Manchester United da Real Madrid da kuma kungiyar shi ta yanzu Juventus. Kuma Pele ya taya shi murnar lashe kofin gasar da yayi sau biyu a jere a shafin shi na Instagram.
Pele ya bayyana a shafin nashi cewa, Ronaldo shine tauraron zamani, wanda yake nuna duk wanda kaga ya samu nasara to dama yana da daidaito kuma yana son abinda yake yi.
Pele ya yabi yan kasar shi na Brazil da suka taimaka wurin lashe kofin gasar kamar su Douglas Costa da Alex sandro da kuma Danilo.
Pele ya kasance masoyin Ronaldo, kuma a kwanakin baya ya bayyana cewa CR7 ya kerewa abokin hammayar shi Messi saboda ya fi shi daidaito, yayin da yake cewa Cristiano shine gwazon yan wasan kwallon kafa na duniya a yau, kuma shima Messi ba za’a manta da shi ba amma shi ba dan wasan gaba bane.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *