Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi ya mamaye jihar Osun yayin dayake yiwa dan takararsu na gwamnan jihar, Larsun Yusuf yakin neman zabe.
Inda ya cewa al’ummar jihar kar su sake maimaita kuskuren da suka yi a baya saboda haka su fito su zabi Labour Party domin a gyara a Najeriya.
Ya kara da cewa gwamnatin yanzu bata biyan albashi, yara basa zuwa makaranta kuma ko gashi babu aikin yi a kasa saboda haka ya kamata su farka.
Labour Party tasu ce saboda kuma ba zata lunkume kudin kasa ba sai dai ta sake gina su yadda ya kamata.