Tsohon gwamnan jihar Anambra dake neman takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar Labour Party, Peter Obi ya yata Atiku Abubakar murna bayan yaci zaben fidda gwani a PDP.
Peter Obi ya kasance daya daga cikin manyan ‘yan takarar dake neman shugaban Najeriya a jam’iyyar PDP kafin ya sauya sheka a watan Mayu.
Kuma shine Atiku ya tsayar a matsayin mataimakinsa a zaben shekarar 2019. A karshe dai Obi yace yana fatan Allah zai taimakawa uban gidansa Atiku yayi nasara.