fbpx
Monday, August 15
Shadow

Pogba ba zai buga gasar kofin duniya ba mai zuwa

Tauraron dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Juventus, Paul Pogba ba zai buga gasar kofin duniya ba wanda za a buga a wannan shekarar a kasar Qatar.

Dan wasan Faransar ya samu rauni a kafar sane yayin da suke yin atisayi da sabuwar kungiyar tasa ta Juventus, kuma daga farko raunin nasa bai yi tsanani sosai ba.

Amma daga bisani kungiyar ta bayyana cewa za a yi masa tiyata kuma zai dauki tsawon wasu lokuta yana jinya, wanda hakan ka iya sawa ya rasa buga gasar kofin duniya.

Karanta wannan  Mun turawa Najeriya sojoji da jakai domin su yaki Biafra, cewar ministan tsaro na jamhuriyar Nijar

Pogba ya koma Juventus ne kyauta daga Manchester United a wannan kakar, bayan ya samu matsala da kungiyar tasa ta gasar Firimiya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.