Kungiyar Kwallon kafa ta PSG ta sanar da daukar tsohon kocin Tottenham, Mauricio Pochettino a matsayin sabon me horas da ‘yan wasanta.
An daukeshine a aikin watanni 18 na farko dan maye tsohon kocin kungiyar, Thomas Tuchel da ta kora daga aiki.
Tun watan Nuwamba na shekarar 2019 Pochettino ke zaune ba aiki bayan korar da Tottenham suka masa.