Friday, July 12
Shadow

Rage kiba cikin gaggawa

Ana iya rage kiba cikin sauri ta hanyar amfani da wadannan hanyoyi:

Yin Azumi

Yin Azumi na daya daga cikin manyan hanyoyin rage kiba sosai, ko kun tuna yanda mutane ke ramewa da azumin watan Ramadana?

To idan mutum na son ramewa ko rage kiba cikin gaggawa, to yayi azumi,ana iya yin Azumin Litinin da Alhamis dan samun sakamako me kyau.

Daina shan Zaki

Idan ana son rage Kiba cikin gaggawa a daina ko a rage shan zaki, watau zaki irinsu lemun kwalba, Yegot/Yoghurt da sauransu.

Ana iya rika amfani da zuma, Mazarkwaila, rake da sauran hanyoyin samun zagi wanda ba na bature ba ko suma ayi amfani dasu saisa-saisa.

Karanta Wannan  Rage kiba cikin sati daya

A rage Amfani da kayan da bature ya sarrafa:

A rage cin kayan da aka sarrafa na roba, leda, da kwalba, a yawaita amfani da kayan da aka hada a gida maimakon na kanti.

Motsa jiki:

Ana iya motsa jiki, irin su gudu, ko tafiya da sauri-sauri, ko daga karfe da sauransu, duk suna taimakawa wajan rage kiba.

Cin Abincin irin su kifi, wake, gyada, Aya, kwai sauna taimakawa wajan rage kiba sosai.

Yana da kyau a rika samun isashshen bacci idan ana son rage kiba cikin gaggawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *