Wednesday, December 4
Shadow

Rage kiba cikin sati daya

Tabbas zaku iya rage kiba cikin sati daya amma abu mafi kyawu shine a shimfida tsari na rage kiba na lokaci me tsawo da yafi sati daya, kalla wata daya, biyu ko uku.

Dalili kuwa shine likitoci sun ce rage kiba a sati daya na iya zamarwa mutum matsala musamman idan yana da wasu manyan ciwuka irin su hawan jini, ciwon suga, ciwon zuciya da sauransu.

Sannan rage kiba a sati daya zai zama ba kitse bane kadai mutum zai rage hadda ruwan jiki da yawan naman jikin mutum wanda hakan ba zai dade ba mutum zai iya komawa yana da kiba.

Amma idan aka bi abun a hakanli, za’a fi samun sakamako me gamsarwa.

Karanta Wannan  Abincin dake rage kiba

Saidai duk da haka,ga masu so, ga yanda za’a iya rage kiba cikin sati daya.

A daina cin abincin da aka sarrafa a kamfani, irin su cakulan, kifin gwangwani, waken gwangwani, yegot, Yoghurt, alawa da biskit da sauransu, a rika cin abincin da aka dafa a gida irin su wake, shinkafa ‘yar gida, Alkama, gero, masara da sauransu.

A daina shan kayan zaki irin su lemun kwalba, Yegot, Ice cream, da sikari wanda ake sayarwa a shago, a koma amfani da zuma da mazarkwaila suma a daidaita amfanin da akw dasu.

A yi azumin kwana 3 a satin.

A rika motsa jiki na tsawon awa 2 a kullun. Idan so samu ne a yi gudu, ko press up, pushups,tsallen kwado, da sauransu.

Karanta Wannan  Maganin rage tumbi

A rika cin kayan ganye irin su zogale,tafasa, latas,lansir.

A sha ruwan lemun tsami a kalla sau biyu da safe a satin, a sha ruwan zogale a kalla sau biyu a satin.

A tabbatar an samu bacci me kyau a cikin satin.

A yi kokarin cin Apple/Tufah, Kifi, Kwai, Aya, gyada, Gujiya, dankali a satin.

Idan aka yi wannan tabbas za’a rage kiba a sati daya.

Amma abin tambaya shine zaka iya ci gaba da tafiya da wannan tsarin rayuwa a kowane sati?

Amsa shine da kamar wuya.

Shiyasa masana kiwon lafiya suka ce ya fi kyau a dauki lokaci me tsawo, wata daya, biyu, 3, 6 ana wadannan abubuwa a hankali dan samun rage kiba me kyau.

Karanta Wannan  Rage kiba cikin gaggawa

Maimakon azumin kwana 3 a sati daya, sai a yi na kwana biyu,litinin da alhamis, maimakon motsa jiki na awa 2, sai a yi na mintuna 30 ko 60 a kullun.

Maimakon shan shayi ko ruwan zogale dana lemun tsami a sati daya, sai a sha su a satuka daban-daban.

Sauran kayan abincin su ma sai a cisu a hankali.

Za’a ga jiki ya daidaita yayi kyau.

Allah ya karemu da lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *