Sunday, May 31
Shadow

Rage kudin mai: Gwamnati na so ta hadamu fada da ‘yan Najeriya>>Masu Gidajen Man Fetur

Kungiyar masu gidajen sayar da man fetur ta Najeriya PETROAN ta joka kan abinda gwamnati ta yi na rage kudin da take basu mai amma bata sanae da kudin da za’a rika sayar da man ba a gidajen man.

 

Gwamnati ta hannun kamfanin mai na kasa, NNPC wanda shine babban me shigo da mai kasarnan ta bayyana ragin kudin da take baiwa masu gidajen mai daga 113.28 zuwa 108. Saidai bata bayyana nawa za’a rika sayar da man a gidajen mai ba.

 

NNPC ba itace ke da alhakin bayyana kudin farashin sayar da mai a gidajen mai ba, PPPRA ce ke da wannan alhakin. Kuma duk da cewa ta yi alkawarin rika bayar da farashin mai a kowane wata amma gashi an yi nisa a watan Mayu, batace uffan ba.

 

Hakan yasa shugaban kungiyar ta PETROAN, Billy Gillis-Harry ya bayyana cewa gwamnatin na so ta hadasu fada da ‘yan Najeriya.

 

Yace gwamnati ta rage kudin da take basu mai daga 113 zuwa 108 kan kowace ganga amma bata bayyana nawa zasu rika sayarwa da mutane ba. Yace idan mutum ya zo sayen mai yasa suna sayarwa a farashin 125 kan kowace lita zai iya musu tambaya kan ragin da aka yi.

 

Yace rashin bayyana farashin da zasu rika sayar da man na nuni da cewa gwamnati ta basu damar sayar dashi duk yanda suka ga dama kenan.

 

Yace sun yi magana da hukumar dake da hakkin kayyade farashin ta PPRA amma har yanzu babu wani abu da aka cimmawa.

 

Saidai yace har yanzu fa akwai wanda ke da man da suka siyo a tsohon farashi dan haka ba lallai a fara ganin canji ba sai sun kammala sayar dashi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *