fbpx
Monday, August 15
Shadow

Rage Talauci: Gwamnatin tarayya za ta fitar da yan Nijeriya Miliyan 40 daga kangin talauci a cikin shekaru 2>>Mista Abdulkarim Obaje 

Gwamnatin tarayya ta ce ta fara kokarin fitar da ‘yan Najeriya miliyan 40 daga kangin talauci ta hanyar Najeriya COVID-19 Action Recovery and Economic Stimulus (NG-CARES), cikin shekaru biyu.

Babban kodinetan shirin na NG-CARES Mista Abdulkarim Obaje ne ya bayyana haka ga manema labarai jiya a birnin Ibadan a yayin rufe taron bita na tsawon mako guda.

Taron horaswar da aka gudanar a Ibadan ya samu mahalarta 440 daga jahohi 36 da babban birnin tarayya Abuja.

Daga cikin mahalarta taron akwai jami’an sa ido da tantancewa (M&E), shugabannin aiyuka a jihohi da kuma sassan kula da lafiya na jihohi a fadin jihohi 36.

Leave a Reply

Your email address will not be published.