fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Rahama Sadau da Maryam Sanda ne aka fi nema a shafukan Internet a 2020

Tauraruwar fina-finan Hausa ta Kannywood Rahama Sadau ce mutum ta huɗu da ta fi tashe a intanet a shekarar 2020 a Najeriya.

Sannan kuma Rahaman ta shiga jerin mutanen da aka fi neman karin bayani a kansu a shafin matambayi-ba-ya-bata na Google a shekarar 2020 a Najeriya, inda ta zo ta tara daga cikin mutum 10.

Kazalika a bayanin da shafin Goggle ɗin ya fitar Maryam Sanda ita ce mutum ta tara cikin goman da suka fi tashe a bana a intanet a Najeriyar.

Shafin Google yakan fitar da kalmomi ko kuma sunayen da mutane suka fi bincikawa a shafin duk shekara a kowace kasa a fadin duniya.

Sannan kuma shafin kan yi wa sunayen rukuni ne, inda ake da rukunan mawaka da wakar kanta da wasanni da ‘yan fim da fina-finan kansu da kuma tambayoyi.

Ga alama dai Rahama Sadau ta shiga wannan jeri ne sakamakon wani abu da ya faru da ita a watan Nuwamban 2020 ɗin, inda aka samu hatsaniya a intanet bayan ta wallafa wasu hotuna tsakanin masu goya mata baya da masu sukarta.

Hotunan da ta wallafa ɗin sun jawo har wasu suka yi saɓo na kalaman ɓatanci ga Annabi Muhammadu, abin da ya jawo babban tashin hankali.

Ita kuwa Maryam Sanda matar da ake zargi da kashe mijinta a 2017, ta shiga jerin ne bayan da a farkon shekarar nan wato a watan Janairu wata Babbar Kotu a Abuja ta zartar mata da hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Maryam ta ɗaukaka ƙara a watan Fabrairu sai dai a watan Disamba Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta tabbatar da hukuncin kisan.

Wataƙila faruwar waɗannan al’amura uku a cikin shkearar ne suka sa Maryam ta zamo cikin waɗanda suka yi tashe a intanet ɗin a Najeriya.

Kazalika, fitacciyar ƴar gwagwarmayar nan Aishatu Yesufu ce ta tara a jerin rukunin tambayoyin da aka fi yi a shafin Goggle a 2020 a NAjeriya.

Aishatu wacce tun 2014 aka san ta da fafutukar ganin an ceto ƴan matan makarantar sakandaren Chibok, ta sake haskawa ne bayan da a watan Oktoba ta shiga cikin zanga-zangar kawo ƙarshen rundunar musamman ta ƴan sanda da ke yaƙi da fashi da makami wato EndSars a Abuja.

Wannan zai iya zama dalilin da ya sa aka dinga neman sanin wace ce ita a shafin Google.

Shi ma zaɓaɓɓen shugaban Amurka Joe Biden ya fito a jerin rukuni daban-daban har uku, na mutanen da suka fi tashe a intenet da waɗanda aka fi neman ƙarin bayani a kansu a Google da kuma rukunin tambayoyin da aka fi yi a Google ɗin.

Jerin mutanen da suka fi tashe a intenet a Najeriya a 2020

1. Joe Biden

2. Rema

4. Rahama Sadau

5. Hushpuppi

6. Laycon

7. Kamala Harris

8. Omah Lay

9. Maryam Sanda

10. Kai Havertz

Mutum 10 da aka fi neman ƙarin bayani a kansu a Google a 2020 a Najeriya

1. Coronavirus

2. US election

3. Joe Biden

4. Google Classroom

5. ASUU

6. Zoom Live

7. Rema

8. Naira Marley

9. Rahama Sadua

10. Hushpuppi

Ko a shekarar 2019 ma tauraruwar fina-finan Hausa Hadiza Aliyu Gabon ta shiga cikin jerin taurarin da aka fi neman karin bayani a kansu a shafin matambayi-ba-ya-bata na Google a Najeriya.

A lokacin ita ma Hadizar ta zamo ta huɗu a jerin na bara baya ga taurarin fim din kudancin Najeriya wato Nollywood, Regina Daniels da Genevieve Nnaji da Tonto Dike, da suke kan gaba.

Wace ce Aisha Yesufu? Tambayoyin da aka fi yi a shafin Google a 2020 a Najeriya

1. Who is the new President of America? – Wane ne sabon shugaban Amurka?

2. When is school resuming in Nigeria? – Yaushe za a koma makaranta a Najeriya?

3. How to make hand sanitizer – Ta yaya ake haɗa man goge hannu na sanitizer?

4. Who is George Floyd? – Wane ne George Floyd?

5. How to make face mask – Ta yaya ake ɗinka takunkumi

6. Who is Joe Biden? – Wane ne Joe Biden?

7. Who is Laycon? – Wane ne Laycon?

8. How to make cake – Yaya ake yin ket

9. Who is Aisha Yesufu? Wace ce Aisha Yesufu?

10. How to make bread – Yaya ake yin burodi?

Waƙoƙin da suka fi tashe a 2020 a Najeriya

1. Davido – Fem

2. Simi – Duduke

3. XXXTentacion – Bad

4. Betty – Butter

5. Rema- Ginger me

6. Rema – Woman

7. Burna Boy – Wonderful

8. Patoranking – Abule

9. Naira Marley – Tesumole

10. Davido ft Nicki Minaj – Holy Ground

Abincin da aka fi neman ƙarin bayani kan yadda ake yin su a Najeriya a 2020

1. Pornstar martini recipe – Yadda ake Pornstar martini

2. Puff puff recipe – Yadda ake fanke

3. Pancake recipe – Yadda ake fankek

4. Red velvet cake recipe – Yadda ake ket me jar kala

5. Meat pie recipe – Yadda ake fanke mit fayif

6. Chin chin recipe – Yadda ake cincin

7. Bread recipe – Yadda ake burodi

8. Chocolate cake recipe – Yadda ake ket

9. Oha soup recipe – Yadda ake miyar Oha

10. Egusi soup recipe – Yadda ake miyar Agushi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.