Rahama Sadau ta saka hotonnan nata tare da wata da suka yi aiki tare a wajan wayar da kai kan yaki da tarin Fuka karkashin majalisar dinkin Duniya.
Rahama ta saka hoton tare da Mawakiyar yankin Larabawa me suna Shabnam Surayo kuma bayyana jin dadin sake haduwa da ita.
Saidai a shafin Twitter, bayan da ta saka hoto, da dama sun rika jawo hankainta da cewa bai dace ba ganin kanta ba a rufe ba da kuma kafadarta a waje.
Saidai duk da haka an samu masu Kare Rahamar.