Tauraruwar fina-finan Hausa, Rahama Sadau ta saka wasu hotunan da suka jawo Mata Allah wada sosai shafukanta na sada zumunta.
A baya dai Rahama kan ce bata damuwa da zagi ko caccakar da ake mata, amma a wannan karin sai gashi bayan shan caccakar sosai, ta cire hotunan.

An ganta a hotunan tare da wasu dan kudancin Najeriya inda tace zasu fara yin fim ne, kuma sun dauki hotunan a kusa da kusa.