Tauraron dan wasan Manchester City, Raheem Sterling yayi bankwana da kungiyar yayin dayake daf da koma abokiyar hamayyarta wato Chelsea.
Sterling ya bayyana cewa yana mika sakon godiyarsa da Kungiyar da kocawanta bakidaya da suka taimaka masa a harkar tamola.
Dan wasan yayi nasarar lashe kofuna bakwai a kungiyar, yayin da yanzu yake shirin komawa Chelsea a farashin yuro miliyan 50.