by hutudole
Cristiano Ronaldo ya aikata abin da hankali ba zai taba dauka ba yayin daya lashe kyautar gwarzon dan wasan shekara kuma ya sadaukar da kyautar wa tauraron dan wasan kungiyar Bayern Munich, Robert Lewandowski a cewar rahotanni.
Manema labarai na kasar Italiya, Tuttusport sun bayyana cewa Jorge Mendez wanda ya kasance wakilin Ronaldo da kuma Lewandowski ya aminta cewa Cristiano ya lashe kyautar gwarzon dan wasan ne a idon jama’a sakamakon yafi Lewandiwski shahara.
Robert Lewandowski yayi nasarar ciwa Bayern Munich da kwallaye 55 a kakar bara kuma ya taimaka mata ta lashe kofuna uku wanda babu wani mashahurin dan wasan daya yi hakan a kakar daga gabata.