Wasu ‘yan gudun hijira daga cikin wadanda hare-haren baya-bayan nan ya rutsa da su a karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna sun koka da rashin ciyar da su a sansanin da aka kebe masu a wasu kanana hukumomi a cikin watan Ramadan.
Wakilan Aminiya da suka ziyarci makarantar Sakandaren gwamnati ta Dokta Shehu Lawal Giwa da ke garin Giwa, inda karamar hukumar ke da sansanin ‘yan gudun hijirar, sun tattaro cewa ana ciyar da su sau daya ne kawai a rana.
Daya daga cikin ‘yan gudun hijirar mai suna Karimatu wadda bazawara ce kuma mahaifiyar ‘ya’ya shida ta ce ana kawo musu abinci da yamma ne kawai a lokacin buda baki amma sai a bar hakan a lokacin a Sahur.
Ta ce da rana ‘ya’yansu da ba sa azumi sai kukan yunwa suke. Yawancin matan sun rasa mazajensu a lokacin da ‘yan bindiga suka mamaye kauyukansu.
Wata bazawara mai ‘ya’ya takwas, Laraba (an sakaya sunanta na gaskiya), ita ma ta koka kan adadin abincin da ake ba su a kullum.
Ta yi kira da a samar da malamai a sansanin don taimaka wa yaransu da ilimi.
Da wakilin Aminya ya tuntubi Daraktan sansanin, Alhaji Idris Saleh Giwa, ya ce karamar hukumar na kokarin samar da abinci ga ‘yan gudun hijirar tun bayan da aka kawo su sansanin makonni biyu da suka wuce.