RAMADAN: ‘Yar Marigayi Sheikh Ja’afar Za Ta Bude Tafsir A Gobe
‘Yar gidan Marigayi Sheikh Ja’afar Mahmoud Adam, Malam Zainab Ja’afar M Adam, za ta fara gabatar da tafsirin Alqur’ani Mai Girma ga mata zalla a Babban Massalacin Juma’a na Uthman bin Affan dake Kofar Gadon Kaya a Birnin Kano.
A Shekarar da ta gabata ne Malama Zainab, ta fara gabatar da tafsiri a masallacin inda mahaifin ta yake gudanar da karattttukan addinin Musulunci.
Daga Abdulrashid Abdullahi, Kano