Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, da Mataimakin sa, Ahmed Wase, sun bukaci musulmai da su yi amfani da watan Ramadana don yin addu’o’i ga kasa.
Sun bayyana hakan ne a sakon ta ya musulamai murnar fara azumtar watan ramadana a ranar juma’a
Sunyi kira da al’ummar musulmi da su yi amfani da wannan lokaci domin rokan Allah madaukakin sarki domin ya kawo karshan wannan annoba data addabi duniya.
Ya yaba da kwazo da sadaukar da kai ga daukacin ‘yan Najeriya dangane da cutar covid-19 inda yayi fatan cewa idan aka ci gaba da addu’o’i, kasar za ta yi nasara kan cutar.