fbpx
Sunday, May 22
Shadow

Ran ‘yan Najeriya da dama ya ɓaci kan dokar hana biyan kuɗin fansa

Baya ga raha da kakaci da tattaunawar ilimi tsakanin ‘yan Najeriya a shafukan zumunta, akwai kuma ɓacin rai kan ƙudirin dokar da ta haramta biyan kuɗin fansa ga masu garkuwa da mutane a ƙasar da Majalisar Dattawa ta amince da ita.

Wannan ba abin mamaki ba ne saboda maganar biyan kuɗin fansa ga ‘yan fashin da ke kamawa da kashe mutane ɗaiɗaikun ‘yan Najeriyar ta shafa kai-tsaye, kuma duk da ƙoƙarin da jami’an tsaro ke yi akasarin waɗanda ake sacewa sai an biya kuɗin ake sako su.

Hukumomi sun yi amanna cewa biyan kuɗin fansar na rura wutar sace mutane a Najeriya, kamar yadda su ma ‘yan Majalisar Dattawan suka yi imani da hakan.

Sai dai kuma ƙudirin dokar, wanda gyaran fuska ne ga dokar yaƙi da ta’addanci, ya tanadi hukuncin kisa ko ɗaurin rai-da-rai ga duk wanda aka samu da laifin garkuwa da mutane.

Kusan kullum, ‘yan Najeriya musamman mazauna yankin arewa maso yamma, na cikin fargabar sacewa ko kisa daga ‘yan fashin daji da ke kai hare-hare a kullum.

Rahoton ya ce alkaluman da aka samu na da nasaba da yadda mahara suka fara amfani da bama-bamai wadanda ake sarrafawa a gida da ake kira IED.

Mutum fiye da 8,000 ne suka yi tsokaci kan labarin dokar da BBC Hausa ta wallafa a Facebook, wasu fiye da 200 kuma suka bayyana ra’ayoyinsu a Twitter. Akasarinsu na ɓacin rai ne da kuma tambayar abin da gwamnati ke yi don daƙile satar ‘yan uwansu.

“Da a ce sun samar da tsaro a ƙasar babu wanda zai so ya tara kuɗi don ya biya fansa,” a cewar ma’abociyar Twitter Surayya Ahmad.

Shi ma wani mai suna Auwal Gambo Ahmad a shafin BBC Hausa na Facebook ya nanata ra’ayin Zainab. yana mai cewa “da kun yi abin da ya dace ai da ba haka ba”.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.