fbpx
Monday, March 1
Shadow

Ranar masoya (Valentine’s Day) ba ranar zinace-zinace ba ce>>Fasto Joshua

Fasto Joshua Olusegun na cocin Christ Reigns Church, Ilorin, a ranar Alhamis ya shawarci matasa da su yi bikin yadda ya kamata a ranar 14 ga watan Fabrairu kuma kada su juya bikin ranar soyayya zuwa taron shashanci.

Fasto Joshua ya ba da wannan shawarar ne a Ilorin lokacin da yake zantawa da manema labarai.

Ya kuma, yawancin mutane suna sun dauki ranar masoya ta duniya a matsayin ranar holewa da yin Jima’i, wannan ba daidai bane.

Ya kuma yi Allah wadai da abin da kananan yara suka aikata na lalata da sunan bikin Valentine, yana mai bayanin cewa bikin ana yin shi ne kawai domin ziyara da kuma faranta wa masoyi ba tare da aikata wani mugun abu ba.

Daga karshe yayi Kira da Malaman addinin Islama da da kirsta da suyi wa’azi domin dakarta da matasa daga aikata wannan mummunan aikin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *