Rarara me kudi ne kawai dai yana so ya nunawa Duniya cewa har yanzu akwai Miliyoyin ‘yan Najeriya masoya Shugaba Buhari>>Ahlan
by hutudole
Tsohon tauraron fina-finan Hausa, Sharif Ahlan ya kare tauraron mawakin Siyasa, Dauda KahutubRarara kan wakar da yace zaiwa shugaban kasa, Muhammadu Buhari inda ya nemi masoyan shuga an kasar da su tara kudi Dubu-Dubu dan yahi wakar.
Ahlan ya bayyana cewa matsalar mutanenmu shine akwai hassada da ganin kashi. Yace Rarara baicewa kowa ya tura masa kudi ba, yace ne masoyan shugaban kasa, Muhammadu Buhari yake magana, yace kuma wannan waka bai ma riga yayi ta ba amma ana ta caccakarsa, wanda hakan yake nuna masu sukar nasa mutanene masu gajeren Tunani.
Yace ai a bari ya saki wakar tukuna a ji abinda zai fada kamin a fara sukarsa. Ahlan yace kamar yansa yakewa ‘yan siyasa Rubuce-rubuce a jaridun turanci yana koresu to haka zaiwa Rarara shima ya gayawa Duniya Muhimmancinsa.