Wasu yan bindiga sun jefa iyalan wani dan kasuwa, Yahaya Hassan Musa cikin bakin ciki bayan sun kashe shi duk da cewa sun karbi kudin fansa naira miliyan shida.
Yahaya Hassan nada aure da yara guda biyu kuma shi mazaunin jihar Kano ne. Yan bindigar sunyi garkuwa da shine a jihar Kogi yayin dawowarsa daga Kotono.
Kaninsa Abubakar Hassan Musa yace wan nasa a jirgin sama yake tafiya koda yaushe, amma kaddara tasa yabi mota a wannan karin. Abubakar ne ya kai masu kudin fansar inda suka fada masa inda zaiga dan uwan nasa amma yaje bai ganshi ba.
Har kwana yayi a cikin dajin kafin daga baya wata mata da akayi garkuwa dasu tare ta fada masa cewa sun kashe shi. Hakan yasa yaje ya samo mafarauta suka nemo gawar suka binne shi a dajin saboda ba motar da zata dauki gawar don ta lalace sosai.