fbpx
Thursday, May 19
Shadow

‘Rashin kyawun hanyoyi na jawowa sojoji tarnaƙi wajen yaki da ‘yan ta’adda a Najeriya’

Wani babban jami’in soja a Najeriya Manjo Janar Christopher Musa, ya ce rashin kyawun hanyoyi da kuma nakiyoyin da ake dasawa na janyo musu tarnaƙi a yakin da suke yi da masu tayar da ƙayar baya kamar yadda Jaridar Punch ta rawaito.

Jami’in sojan ya ce, “Mun cire nakiyoyi fiye da 98 zuwa yanzu, sannan har yanzu ba mu fidda ran samun wasu ba.

“Za ka yi mamaki tsakanin Maiduguri zuwa Monguno a jihar Borno, tafiya ce mai nisan kilomita 180, amma sai ka sauka kasa ka gyara hanya ko ka sauka daga kwalta saboda rashin kyawun hanya.”

Karanta wannan  Suna jima'i damu kamar dawaki, kuma suna shan miyagun kwayoyi sosai>>Wata Tsohuwar matar 'yan Boko Haram

Manjo Janar Musa, ya bukaci gwamnati da ta taimaka ta gyara hanyoyin da suka lalace domin bai wa sojoji damar gudanar da ayyukansu yadda ya dace.

Jaridar Punch, ta rawaito babban jami’in sojan na cewa masu tayar da kayar da baya akalla 11,000 sun miƙa wuya bayan irin ayyukan da rundunarsu ta yi a yankin na arewa maso gabashin Najeriyar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.