fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Rashin Lafiya ta tilasta Anthony Martial barin wajan Atisayen Manchester United

Antony Martial ya rasa wasan da Manchester United ta lallasa Southampton 3-2 a gasar Premier league ranar lahadi duk da cewa ya ziyarci filin, sakamakon ya kamu da rashin lafiya.

Kuma a safiyar yau ma haka,  rashin lafiyar tasa ya bar filin atisayi bayan mintina 11 kacal yayin da United take shirye shiryen tarbar kungiyar PSG a filinta na Old Trafford ranar laraba a gasar zakarun nahiya turai.

Shima golan baban golan kungiyar, David De Gea ya samu rauni yayin da suke karawa da Southampton jiya,amma manajan kungiyar Ole Gunnar ya bayyana cewa yar buguwa ce yayi kuma zasu yi mai gwaji domin tabbatar da lafiyar shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published.