fbpx
Saturday, May 28
Shadow

Rashin Tausai: ‘Yan Bindiga sun harbi ‘yar shekara 2 a al’aurarta, tana Asibiti rai hannun Allah

‘Yan Bindiga da suka kai hari jihar Benue sun harbi wata yarinya me shekaru 2 a Duniya a  Al’aurar ta inda take can Asibiti rai hannun Allah.

 

Msurshima Iorshie na can asitin koyarwa na jami’ar jihar Benue inda take jinya.

 

Ranar Litinin ne ‘yan Bindigar suka kai hari garin Tiortyu dake karamar hukumar Tarka a jihar ta Benue.

 

Akalla mutane 15 ne suka mutu a hari  inda kuma wasu da dama suka jikkata.

Mahaifiyar yarinyar, Mrs. Faith Iorshie ta bayhana cewa sun tafi gona ita da mijinta suka bar yarinyar a wajan kakanta inda daga nan ne kuma suka samu labarin maharan.

Karanta wannan  'Yan Bindiga sun kashe Delegates 3 a jihar Naija

 

Tace sun ruga kamin su kai gida har maharan sun kai kauyen sun kuma kashe kakan yarinyar inda ita suka harbeta a al’aurarta.

 

Tace sun kaita Asibiti bayan da suka ga bata mutu ba tana numfashi.

 

Daya daga cikin ma’aikatan Asibitin yace yarinyar na nuna alamun samun sauki amma sai an mata aiki na musamman kamin al’aurarta ta dawo daidai.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.