fbpx
Monday, December 5
Shadow

Rashin tsaro: Mambobin majalisar wakilai sun bukaci NSA da ministan tsaro su yi murabus

Wasu ‘yan majalisar wakilai sun bukaci ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Manjo Janar Babagana Monguno su yi murabus bisa zargin gazawa wajen gudanar da ayyukansu.

Hakan ya biyo bayan gabatar da kudurori biyu kan muhimman batutuwan da suka shafi jama’a cikin gaggawa yayin zaman majalisar a ranar Laraba 13 ga watan Afrilu.

Yusuf Gagdi (APC, Plateau) da John Dyegh (PDP, Benue) sun yi tir da kisan da wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka yi a mazabunsu a kwanakin baya.

Da yake jawabi yayin zaman majalisar, Gagdi ya ce an shirya kai hare-haren ne saboda akwai gargadin farko da hukumomin tsaro suka yi watsi da su bayan an sanar da su.

John Dyegh a nasa bangaren, ya bayyana cewa kimanin mutane 19 ne aka kashe a wasu al’ummomi biyu tsakanin ranar Litinin da safiyar Talata. Ya yi nuni da cewa hare-haren na zama akai-akai wanda hakan na iya kara ta’azzara halin da jihar ta Benue ke ciki.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *