Wata ‘yar takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Ibinabo Dokubo, ta koka da yadda matsalar tsaro ke kara tabarbarewa a kasar.
Matar wadda take fatan zama shugaban kasa ta ce rashin tsaro musamman a yankin Arewa maso Gabas da Arewa ta tsakiya ya sanya ‘yan Najeriya ba su ga dimbin nasarorin da gwamnatin tarayya karkashin jam’iyyar APC ta samu, musamman a fannin samar da ababen more rayuwa.
Ta yi wannan magana ne a lokacin da ta bayyana kudurinta na tsayawa takarar shugaban kasa jiya a Abuja.
Dokubo ta ce za ta nemi tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyya mai mulki tare da jiga-jigan jam’iyyar irinsu Bola Tinubu da Gwamna Yahaya Bello da sauran masu neman kujerar.