Wednesday, January 21
Shadow

Rashin tsaro: Tinubu na ganawa da shugabannin hukumomin tsaro na ƙasa

A halin yanzu shugaba Bola Ahmed Tinubu ya na wata ganawar sirri da shugabannin hukumomin tsaro da kuma babban sufeton ƴansanda na kasa (IGP) a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

DAILY TRUST ta rawaito cewa wadanda su ka halarci ganawar sun hada da babban hafsan tsaron kasa, Janar Christopher Musa; Babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede; Hafsan Hafsoshin Sojan Sama, Air Marshal Hassan Abubakar; Babban Hafsan Sojin Ruwa, Vice Admiral Emmanuel Ogalla; da Sufeto Janar na ƴansanda, Kayode Egbetokun.

Ko da ya ke ba a fayyace cikakken bayanin taron ba har zuwa lokacin da Trust ta buga labarin, amma tattaunawar ba za ta rasa nasaba da sabbin hare-haren ƴan ta’adda a wasu sassan kasar ba.

Karanta Wannan  An Samu Wasu Marasà Tausayì Sun Jefa Wannan Dattìjò Cikin Zulumi, Inda Aka Biyo Dare Aka Kwashe Masa Kan Kekunan Dinkin Da Yake Lallaba Rayuwarsa Da Su

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *