Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ce wasu gwamnoni a kasar ba su damu da ayyukan su ba a matsayin su na manyan hafsoshin tsaro na yankunansu.
Bello, wanda bai bayyana sunayen irin wadannan gwamnonin ba, ya ja kunnen su da cewa a kodayaushe suna zuwa wurin Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), lokacin da ya fuskanci kalubalen tsaro kamar fashi da makami, satar mutane, rikicin manoma da makiyaya, rikicin kabilanci. wasu.
Gwamnan jihar Kogi ya yi wannan maganar ne a ranar Alhamis yayin da yake zantawa da manema a cikin wani shiri mai suna ‘Sunrise Daily’ na gidan talabijin.
Bello ya kumace wasu gwamnoni a kasar suna wasa da rayukan ‘yan kasar nan saboda siyasa.