fbpx
Wednesday, June 29
Shadow

“Rashin zabarmu da APC tayi ka iya sa ta fadi zaben shekarar 2023”>> Kungiyar Inyamurai ta Ohaenaze Ndigbo

Kungiyar inyamurai ta Ohanaeze Ndigbo ta bayyana cewa rashin zabar dan kudu maso gabashin Najeriya da APC tayi a zaben fidda gwani ka iya taki yin nasarar lashe zaben shekarar 2023.

Kungiyar Inyamuran ta bayyana hakan ne biyo nasarar da Asiwaju Bola Ahmad Tinubu yayi na lashe zaben fidda gwani na APC.

Wanda yayi nasarar samun kuru’u 1271, sai Amaechi yazo na biyu da kuru’u 316 sai farfesa Yemi Osinbajo yazo na uku da kuru’u 235.

Yan takarar kudu maso gabashin Najeriyar da suka samu kuru’u sosai a zaben sun hada da gwamnan Ebonyi, David Umahi wanda ya samu kuru’u 38 sai tsohon ministan Ilimi Chukuemeka da Christopher suka samu daya-daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.