fbpx
Saturday, August 20
Shadow

Rasuwar Dakta Ahmad ta girgiza ni>>Ganduje

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya baiyana cewa rasuwar fitaccen malamin addinin Musluncin nan , Dakta Ahmad Muhammad Bamba, ta girgiza shi da ma al’ummar Kano baki ɗaya.

Ganduje ya baiyana haka ne a sakon ta’aziya ta hannun kakakin sa, Abba Anwar a yau Juma’a.

“Mutuwar sa ta girgiza Kano matuƙa. Hamshaƙin malami ne da ya ke da ɗumbin ilimin addini. Malami ke da ya ke da sani mai zurfi a kan Hadisan Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama.

“Malami ne da ya ke amfani da majailisin karatun sa wajen yaɗa zaman lafiya tsakanin al’umma da ɗarikun addini.

“Wannan rasuwa ce da mu ke alhinin ta kuma za mu dade mu na alhini da jimami,” in ji Ganduje.

Karanta wannan  Tuna baya: Tinubu ya taba cewa al'ummar Najeriya Obasanjo shugaban masu magudin zabe a tarihi

Ganduje ya yi kira ga sauran malami na jihar da su kwaikwayi irin aiyukan da ya yi wa addinin Musulunci.

“Ya kafa tushe mai ƙarfi na kiran al’umma da su karɓi addinin musulunci kuma malami ke mai aikata abubuwan da ya ke yin wa’azi a kai,”

Ganduje ya mika ta’aziyar sa ga iyalin mamacin, sannan ya yi addu’ar Allah Ya yi masa rahma , Ya kuma baiwa iyalin sa da mutanen Kano jure rashin sa.

Daily Nigerian

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.