Kiristoci da fastocinsu na Najeriya sun koka kan harin da ‘yan bindiga ke cigaba da kaiwa coci da kuma garkuwa da malamansu a fadin kasar nan.
Yayin da a juma’ar data gabata cocin katolika ta gudanar da jana’izar mutane 40 da ‘yan bindiga suka kaiwa hari suka kashe a Owo jihar Ondo.
Kuma fastoci da dama suna hannun ‘yan bindigar a halin yanzu suna bukatar a basu makudan kudade kafin su sake su.
Wani faston cocin RCCG a babban birnin tarayya ya bayyana cewa mutane sun daina zuwa coci sosai tunda aka kashe kirista 40 a jihar Ondo.
Kuma wannan harin su kadai ake kaiwa domin ba zaka taba jin cewa an kai hari masallaci ba ko kuma wurin bautar Musulmi ba.