fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Rb Leipzig ta cire Tottenham, Atalanta ta cire Valencia daga gasar Champions League

Kungiyar kwallon kafa ta RB Leipzig ta lallasa Tottenham da ci 3-0 a wasan da suka buga na daren Talata na gasar cin kofin Champions League.

 

Dama dai a wasan farko da suka buga RB Leipzig ce ta ci Tottenham da kwallo 1-0, yanzu ta ci jimullar kwallaye 4-0 kenan, wanda da wannan sakamako ne RB Leipzig ta wuce zuwa matakin Quarterfinals inda ita kuma Tottenham ta fita daga gasar.

 

Kocin RB Leipzig,  Julian Nagelsmann dan shekaru 32 shine koci mafi karancin shekaru da ya taba kaiwa wasan quarterfinals na gasar Champions league, sannan a lokacin da Mourinho ya ci kofin Champions league na farko da FC Porto yana da shekaru 16 ne.

 

Wasanni 6 kenan a jere Tottenham ta buga ba tare da yin nasara ba. Wannane karin farko da haka ta faru da Mourinho a tarihinsa.

 

Itama Atalanta ta cire Valencia daga gasar bayan lallasata da ci 3-4 a yau,  a wasa na farko ma 4-1 Atalanta ta mata wanda hakan ke nufin taci jimullar kwallaye 8 kenan.

 

Dan wasan Atalanta, Jocip ilicic ya kafa irin tarihin da Messi ne da Ronaldo kawai ke dashi inda yaci kungiya 1 kwallaye 5 a gasar Champions League. Hakanan dan shekaru 32 ya kafa tarihin zama dan kwallo mafi tsufa da ya ci kwallaye 4 a wasan Champions League 1. Kaminshi Ibrahimovic ne ke da wannan tarihi

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.