Sunday, June 7
Shadow

Real Madrid na ganin Mbappe ne kadai zai maye mata gurbin Ronaldo, Saidai PSG ta mai karin Albashi dan ya ci gaba da zama

A kowace shekara kungiyar Real Madrid suna kokarin siyan manyan yan wasan kwallon kafa kamar yadda suka siya zakaran Chelsea Hazard wanda yasa kungiyar chelsea suka yi nasara a gasar Europa lig da kuma champions lig.

Kuma Madrid suna da ra’ayin siyan tauraron PSG wato Neymar amma dan wasan baida ra’ayin shiga kungiyar Real yafi so ya koma kungiyar shi ta Barca. Madrid sun kara harin wani zakaran psg wato Mbappe kuma har yanzu suna kokarin siyan dan wasan.
Mbappe yana kokari sosai a matsayin mai shekaru 21 kuma yaci kwallaye guda 18  kuma ya taimaka wurin cin kwallaye guda 5 a wasanni guda 20 daya buga a kakar wasan bana. Masoyan real Madrid sun ce Mbappe ne kadai zai iya maye masu gurin Cristiano Ronaldo.
Ana sa ran cewa dan wasan zai iya zama zakaran yan wasan kwallon kafa na duniya nan bada dadewa ba kuma zai fi dacewa da real Madrid amma PSG na kokarin karawa Mbappe albashi don yayi burus da sabuwar kwangilar da real Madrid suke kokari yi mai. Kuma suma Madrid suna kokartawa dan suga cewa sun shawo kan dan wasan.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *